
Labaranyau ta samu labarin cewar Adam A Zango yayi aure har sau shida a baya Amina, Aisha, Maryam, Safiya, da Ummul Kulsum, ya nada ‘ya’ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar din da ya aura kafin su rabu.
Wannan labari zai duba rayuwar Adam A Zango da matansa 6, tare da bayyana gaskiya, jita-jita, da wasu abubuwan da mutane da yawa ba su sani ba.
Adam A Zango: Tauraro Mai Hazaƙa
An haifi Adam A Zango a garin Zango, jihar Kaduna. Ya shahara a fagen fina-finai tun shekaru da dama da suka gabata, inda ya taka rawa a matsayin jarumi, mawaki da kuma mai shirya fina-finai. Dukkan wadannan sun kara masa suna da daukaka a tsakanin masoya fina-finai na Hausa.
- Instagram: @adam_a_zango
- Facebook: Adam A Zango
- TikTok: @iam_adam_a_zango
- Twitter: @princeazango
- YouTube: Adam A. Zango Official
Rayuwar Adam A Zango da Matansa Amina, Aisha, Maryam, Safiya, da Ummul Kulsum
Adam A Zango yayi aure har sau shida, inda ya auri Matansa Amina Uba Hassan, Aisha, Maryam, Maryam Abdullahi Yola, Ummul Kulsum da Safiya Umar Chalawa. Ga cikakken bayani akan matansa:
1. Amina Uba Hassan

Adam A Zango ya auri Amina Uba Hassan ne a shekarar 2006, kuma sun haifi ɗa namiji mai suna Haidar a shekarar 2008.
Bayan watanni biyar da haihuwar ɗansu, wato a cikin shekarar 2008, suka rabu.
Kana Bukatar: Amina Uba Hassan Biography | Education, Net Worth, Movies, Husband
3. Aisha
Zango ya kara auren wata matar mai suna A’isha, ‘yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna. Ta haifa masa ‘ya’ya maza uku
3. Maryam
Adam A Zango ya auri matar sa ta uku ne mai suna Maryam daga jihar Nasarawa bayan ya rabu da A’isha.
2. Maryam Ab Yola

Adam A Zango ya auri Maryam Abdullahi Yola a ranar Asabar, 15 ga Yuni, 2013, a masallacin Juma’a na Izala da ke Lubge, Abuja, kan sadaki naira dubu 50 lakadan ba ba ajalan ba.
Bayan auren, Maryam ta koma gidansa a Kaduna. Duk da haka, a ranar 30 ga Satumba, 2022, Maryam ta sake yin aure, inda ta wallafa bidiyoyin bikin a shafinta na Instagram.
Kana Bukatar: Maryam Ab Yola Biography | Education, Net Worth, Movies, Husband
5. Ummul Kulsum

Adam A Zango ya auri Ummul Kulsum, ‘yar asalin garin Ngaoundere a Jamhuriyar Kamaru, a shekarar 2015.
Ita ce ta fara haifa masa diya mace, wacce ya sanya mata suna Murjanatu.
Duk da haka, mun samu rahotannin cewa Ummul Kulsum, mahaifiyar Murjanatu, ta sake yin aure a wani lokaci bayan rabuwarsu
4. Safiya Umar Chalawa

Adam A Zango ya auri Safiya Umar Chalawa a shekarar 2019, a Fadar Sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi.
Sun rabu a shekarar 2023, bayan kusan shekaru hudu tare. Rahotanni sun nuna cewa rikici ne ya addabi aurensu, wanda ya kai ga Safiya ta yi yaji, kuma Adam a Zango ya bata takardar saki don gudun kada a kai batun kotu.
Domin ƙarin bayani, zaku iya kallon wannan bidiyon:
Gaskiya da Jita-jita Akan Rayuwar Auren Adam A Zango
An dade ana yayata labarai da jita-jita game da rayuwar auren Adam A Zango, inda wasu ke ganin cewa yana da son mata da yawa, wasu kuma suna ganin cewa yana da matsalar zama da mata ne.
Sai dai a cikin wata hira, Adam Zango ya bayyana cewa yana da burin samun kwanciyar hankali a rayuwar aure, amma yana fuskantar kalubale kamar kowane namiji.
Kana Bukatar: Adam A Zango Biography | Education, Net Worth, Movies, Wife

Yayen Adam A. Zango
- Haidar
- Osama
- Hauwa
- Fadila
- Faisal
Yana kokarin kula da yaransa, kuma ya bayyana cewa yana matukar kaunarsu duk da matsalolin aurensa.
Abubuwan da Baka Sani Ba Game da Rayuwar Aurensa
- Adam A. Zango yana da yara daga matansa daban-daban, kuma yana kokarin kula da su.
- Duk da cewa yana da aure sau da yawa, yana kokarin ganin ya samu kwanciyar hankali da farin ciki.
- Ya bayyana cewa matsaloli ne suka hana auren nasa dorewa, amma yana fatan samun wadda za ta tsaya masa har abada.
Q&A
Sau nawa Adam A. Zango ya taba yin aure?
Ya yi aure sau biyar, inda ya auri mata daban-daban a lokuta daban-daban.
Wasu mata Adam A. Zango ya aura?
- Amina
- Maryam
- Maryam
- Aisha
- Safiya
- Ummi
Me ya sa auren Adam A. Zango bai Jimawa?
A cewar wasu rahotanni da kuma bayanansa, matsalolin rayuwa da rashin fahimtar juna sun taka rawa wajen kawo ƙarshen aurensa da matansa.
Yara nawa Adam A. Zango ya haifa?
- Haidar
- Osama
- Hauwa
- Fadila
- Faisal
Shin Adam A. Zango yana kula da yaransa?
Eh, yana kokarin kula da yaransa, kuma ya bayyana cewa yana matukar kaunarsu duk da matsalolin aurensa.
Me yasa rayuwar auren Adam A. Zango ke jawo cecekuce?
Saboda kasancewarsa shahararren jarumi, mutane suna bibiyar rayuwarsa sosai, musamman bangaren aurensa da matansa.
Shin Adam A. Zango yana da niyyar sake yin aure?
Ya bayyana cewa yana da burin samun kwanciyar hankali a rayuwar aure, kuma yana fatan samun wadda za ta tsaya masa har abada.
Kana Bukatar: Cikakken Jerin Finafinan Ali Nuhu Tun Daga Farkon Acting Dinsa Zuwa 2025
A Karshe
Rayuwar aure a duniya tana da nasarori da kalubale. Adam A. Zango ya kasance tauraro da mutane da yawa ke bibiyarsa, kuma hakan yana sanya duk wani motsinsa ya zama abin magana. Duk da haka, yana kokarin zama mutum mai kyau kuma yana fatan samun kwanciyar hankali a rayuwarsa ta aure.
Wannan labari ya yi bayani akan matansa, gaskiya da jita-jita, tare da abubuwan da mutane da dama ba su sani ba. Me kake tunani game da rayuwar aurensa?
Ga cikakken bayyani nan a cikin faifan bidiyo