Girke Girke

Yanda Ake Gwaten Filanten, Soyayyen Filanten Da Kwai (Plantain Porridge)

Mafi yawan lokuta amfani jin dadin plantain idan aka soya shi, ko a tafasa shi ko a gasa shi a ci da sauce. Paten Plantain Yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa. Ita wannan abinci anfi ci kudancin Najeriya.

Kayan Hadi

Danyen Plantain (Manya 5 ko kanana 8)
Nunannen Plantain (Manya 4 ko kanana 6)
Kabewa Dan daidai
Alaiyaho na 100 Naira
Albasa babba guda daya
Crayfish Kofi daya
Manja rabin kofi
Maggi
Busashshen Kifi
Nama
Attaruhu

Yadda Ake Hadawa

Da farko za a wanke a fere plantain, kamin nan an saka nama a wuta Dan ya tafasa da kayan kanshi ciki har sai yayi laushi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Sannan a yanka plantain daidai girman da ake so, sai a saka a wuta a zuba su manja, attaruhu, crayfish, maggi da Dan gishiri kadan.

Sai a barshi ya dahu na Dan wani lokaci, sai a zuba busashshen kifin sai a juya shi da ludayi.

Sannan a zuba Alaiyahu a barshi yayi minti biyar. Sannan a sauke
Sai a zuba a faranti da nama mai dadi.

Lallai za ayi santin wannan girki.

Soyayyen Filanten Da Kwai (Fried Plantain with eggs)

Shi wannan abinci na marmari ne Wanda akeci a duk fadin najeriya. Daga gidaje har wajen siyar da abinci anayi kuma Yana da saukin hadawa ga marasa aure.

Kayan Hadi

Nunannen Plantain Guda biyu
Koyi guda daya
Piya
Man gyada
Gishiri

Yadda Ake Hadawa

Da farko za a fere plantain sai a yanka, sai a Dan watsa Gishiri kadan a kan plantain din da aka yanka, sai sanya frying pan akan wuta a zuba mangyada, in yayi zafi sai a zuba plaintain a ciki sai a rage zafin wutan kadan Dan ya soyu da kyau. Har sai yayi jajawur kamin a sauke.

Sai a fasa kwai a cikin dan karamin kwano
A yanka albasa da attaruhu ciki in Ana bukata da dan maggi. A kada da kyau
A sanya frying pan a wuta a zuba man gyada cokali daya ko rabin cokali in yayi zafi sannan a zuba kwan a soyashi da kyau.

Sai a zuba plantain din da aka soya a plate, a saka soyayyen kwan a cikin plate din sai a gyara piya shima a saka a shirya shi.

A ido Yana da kyau haka a dandano.

Yanda Ake Asillen Kwadon Zogale

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button