EntertainmentLabaran Yau

Tauraruwa Maryam Yahaya Ta Dawo Masana’antar Fim Gadan Gadan

Tauraruwa Maryam Yahaya Ta Dawo Masana’antar Fim Gadan Gadan

Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood, Maryam Yahaya ta dawo fim bayan ta murmure daga matsananciyan rashin lafiya da ta yi fama da ita.

A 2021 jarumar ta fara rashin lafiya, inda ta yi matukar ramar da har ya kai ga ba kasafai ake bari ana ganinta ba.

Maryam dai a lokacin tafito tayo hira da kafan yada labarai, ta ce tana fama ne da malariya da typhoid, rashin lafiyar ta sha fama da jinya har ake ganin da wahala ta dawo masana’antar. A watan baya, jarumar ta yi tafiya zuwa Dubai domin shakatawa, inda ta rika hotuna da dama, da har wasu daga cikin hotunan suka jawo ce-ce-ku-ce.

Yanzu haka mawalafin Labaranyau ya riski bayanin Aminiya yanda ta bada cikakken tabbaci a cewa jarumar ta samu murmurewa daga jinyan tasha, kuma ta dawo harkar fim, inda a yanzu haka take cikin jaruman da za su fito a  fim din Alaqa zango na biyu.

Alaqa dai fim ne mai dogon zango na kamfanin FKD Production na Ali Nuhu, wanda dama shi ne ubangidanta a masana’antar.

A bara ne fitaccen mai rubutu a Facebook, Datti Assalafy, ya rubutu a shafinsa, yana kira ga kungiyoyin kare hakkin mata na duniya su kawo wa Maryam Yahaya dauki, inda ya yi zargin cewa abokan sana’arta sun ruguza mata rayuwa, sannan sun mayar da ita wajen iyayenta sun kyamace ta, ko ziyartarta ba sa yi.

Ya ce a rubutun, “Wannan cin zarafi ne da keta hakkin rayuwar mata dangin rauni, ba a haka ’yan Hausa fim suka dauke ta a gidan mahaifinta ba. Mahaifinta ba ya da karfin daukar lauyoyin da za su kwato mata ’yanci a biya ta diyya, tunda sun kashe mata rayuwa.”

Sai dai tun a lokacin masu ruwa da tsaki a harkar suka masa rubdugu, inda suka ce maganarsa zuki-ta-malle ce kawai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button