Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Farfesun Kifi

Hanya mafi sauki dan hada farfesun kifi muka kawo muku. In an bi sharudodin bara a ji kunya ba wajen dafa farfesun kifi Mai dandano.

Biyoni domin samun cikakken bayanin yanda ake girka farfesun kifi.

Kayan Hada Ferfesun Kifi

1. Kifi (tarwada)danye

2. Lemon tsami

3. Citta

4. Tafarnuwa

5. Masoro

6. Gyadan inyamurai

7. Attaruhu da albasa

8. Maggie

9. Gishiri

Farfesun Kifi Cikin Karamin Lokaci
Farfesun Kifi Cikin Karamin Lokaci

Yanda Ake Girka Ferfesun Kifi

  • A wanke kifin da kyau saboda cire karni zaayi amfani da lemon tsami a goga dakyau ajikin kifin awanke dashi sai asa a tukunya
  • A daka citta, tafarnuwa, masoro, gyadan inyamurai, attaruhu da albasa a zuba akan kifin asa Maggie da gishiri sannan a zuba ruwa a daura a wuta sai a rufe tukunyar
  • Bayan wasu mintuna kamshin zai fara tashi alamun ya fara nuna sai a barshi kaman na minti biyu zuwa uku sai a sauke baa son ana jujjuyawa saboda zai farfashe.
  • Idan ma wani kifinne ba tarwada ba duk Hakan zaayi ferfesun.
Farfesun Kifi
Farfesun Kifi

A ci dadi lafiya.

Ga Bidiyon Yanda Ake Ferfesun Kifi Daga Bisani


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading