Duk da irin nasarorin da suka samu, wasu daga cikin masu bibiyar Kannywood sun yi ta zargin cewa akwai matsala tsakanin Ali Nuhu da Adam A Zango.
Wasu suna ganin cewa takun sakarsu ta samo asali ne daga gasa da ke tsakaninsu, yayin da wasu ke tunanin akwai wani sirri da bai bayyana ba.
A wani lokaci, an ji cewa Adam A Zango ya fice daga cikin tafiyar FKD (kamfanin Ali Nuhu), lamarin da ya sa ake ganin cewa sun samu sabani tsakanin su ne.
Sai dai, daga bisani, an gansu tare a wasu fina-finai, wanda hakan ya nuna cewa ko dai sun sasanta ko kuma ba su taɓa samun masala tsakaninsu ba tun farko.
Sai dai, duk da shahara da nasarar da suka samu, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce:
Menene gaskiyar dangantakar su?
Shin akwai matsala a tsakaninsu ko kuwa kawai jita-jita ce?
A wannan rubutu, za mu tonawa masu karatu gaskiya asirin alakar Ali Nuhu da Adam A Zango – sabanin abinda aka sani ko ake zato!
Sirrin Alakar Ali Nuhu Da Adam A Zango – Sabanin Abunda Ya Bayyana
Ali Nuhu da Adam A Zango sun kasance manyan jarumai a masana’antar Kannywood, kuma sun sha yin takun saka a baya.
Akwai labarai da ke nuna cewa sun samu sabani a shekarar 2015 saboda wani rikici da ya shafi Rahama Sadau.
Duk da haka, sun yi sulhu a shekarar 2018 bayan wata babbar rikici ta sake barkewa.
A yanzu, ana ganin sun samu kyakkyawar alaka, kuma sun ci gaba da aiki tare a wasu fina-finai;
Wannan yana nuna cewa duk da sabanin da suka samu a baya, sun iya shawo kan matsalolin su kuma sun ci gaba da aiki tare don ci gaban masana’antar Kannywood.
Sirrin Alakar Ali Nuhu Da Adam A Zango – Sabanin Abunda Ya Bayyana
Tarihin Dangantakar Ali Nuhu Da Adam A Zango
Dangantakar Ali Nuhu da Adam A Zango tana ɗaya daga cikin dangantaka mafi karfi a masana’antar Kannywood.
Wa’innan taurari biyu sun taka rawar gani sosai a harkar fim, sun kuma kasance a sahun gaba wajen samar da fina-finai masu ma’ana da jan hankali.
Sai dai, kamar yadda aka saba a kowace masana’anta, kasancewar taurari biyu masu ƙarfi tare a tafiya daya kan jawo gasa, jita-jita, a kuma wasu lokutan ƙarin kwaazo kan alaƙarsu.
Ali Nuhu yana cikin waɗanda suka kafa tubalin fina-finan Hausa na zamani.
Tun daga ƙarshen shekarun 1990, ya kasance babban jarumi, darekta kuma furodusa.
Adam A Zango kuwa, ya fara ne a matsayin me editin bidiyo kafin daga baya ya zama jarumi.
A farkon shekarun 2000, ya sami damar shiga masana’antar Kannywood, kuma Ali Nuhu ya kasance cikin mutanen da suka taimaka masa wajen samun matsayi a fim.
A wannan lokaci, suna da kyakkyawar alaƙa, suna yin fina-finai tare, kuma ana ganin kamar Ali Nuhu na cikin manyan da ke tallafa wa Adam A Zango a tafiyarsa.
Sirrin Alakar Ali Nuhu Da Adam A Zango – Sabanin Abunda Ya Bayyana
Lokacin Da Alaƙarsu Ta Karfafa
A tsakiyar shekarun 2000, Ali Nuhu da Adam A Zango sun shahara sosai a Kannywood kuma sunyi fina-finai da dama tare.
kamar su:
Sultana
Izzar So
Alaqa
Gwaska
Gwaska Return
Dan Marayan Zaki
Zuma Da Madaci
Hisabi
Nas
Balarabe
Dare Daya
Sai Wata Rana
Ruf Kofa
Sun kara tabbatar da cewa suna da kwakkwaran haɗin gwiwa.
A wannan lokaci, su biyun sun yi fina-finai da dama tare, suna kuma nuna goyon baya ga juna.
Me Ya Sa Masoya Ke Ci Gaba da Tunanin Akwai Matsala?
Duk da cewa babu wata hujja da ke tabbatar da gaba a tsakanin su, har yanzu wasu masoya na ganin cewa Ali Nuhu da Adam A Zango ba su da alaƙar da suke da shi a baya.
Dalilan da suka sa ake jin haka sun haɗa da:
Ba sa fitowa tare a fina-finai kamar da.
Ba sa yawan yin hira da juna a kafafen sada zumunta.
Ba sa goyon bayan juna a yawancin abubuwan da suka shafi masana’antar.
Sai dai kuma, har yanzu ba a taɓa ji daga bakinsu cewa suna gaba da juna ba, wanda hakan ke nufin akwai yiyuwar kawai masoya ne ke cusa tunanin cewa suna da matsala.
Sirrin Alakar Ali Nuhu Da Adam A Zango – Sabanin Abunda Ya Bayyana
Daga Karshe
A takaice dai, dangantakar Ali Nuhu da Adam A Zango ta yi matuƙar ƙarfafa a baya, amma daga bisani, sai aka samu wata rashin jituwa (ko kuma tazara) da har yanzu ba a san dalilinta ba.
Koda yake ba a jin su suna zagin juna, babu sabawa tsakanin su kamar yadda aka sani a baya.
Sai dai, hakan ba yana nufin cewa suna gaba da juna ba.
Ana iya cewa kawai kowannensu ya koma kan tafiyarsa ne.
Me Kuke Gani?
Shin kuna ganin akwai matsala tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango?
Ku bayyana ra’ayinku a cikin comments!
Ku bibiye shafinmu don samun sabbin labarai masu kayatarwa!