Labaran Yau

Na’urar Tantance Zabe Yazo Ya Zaunane Cewar Atiku

Na’urar tantance Zabe yazo ya zauna cewar Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yace na’urar tantance wa yayin zabe yazo ya zauna domin ingancin ta wajen tantance wa da bayyana sakamakon zaben ta hanyar Zamani a Najeriya.

Atiku, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben fabrailu da ta gabata, yayi jawabi wanda ta fito ta ofishin sadarwansa a Abuja ranan talata.

Yayi bayanin ne a sakamakon nasara da gwamnan Osun Ademola Adeleke yayi kan zaben Gwamna wanda akayi karar a babban kotun Najeriya.

DOWNLOAD MP3

“Duka Mun shaida kan lamarin da yazo na zabe wanda akayi da na’urar tantance wa BVAS, hakan ya taimaka wajen hukuncin kotu.

“Dokokin da akawo ya taimaka wajen bawa mutane karfin zaben wanda suke so, yan siyasa da ke tunanin zasu iya badakala a harkan zabe sun fahimci yanzu karfin demokradiyya tafi abin wasa”

Shi Atiku ya ce yan Najeriya su rungumi cigaban da aka samu ta hanyar demokradiyya a kasar.

DOWNLOAD ZIP

“Mu daina daukar doka a hannun mu, mu kasance masu yin abinda ya dace, yin abinda ya dace shine yancin mu”.

Abubakar Atiku ya taya mutanen jihar Osun murnan nasara da jajircewa wajen bawa Adeleke karagan mulki.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button