Labaran Yau

Jami’ar Al-qalam Ta Samu Lasisin KosaKosai Goma Sha Uku

Jami’ar Al-qalam ta samu lasisin kosakosai goma sha uku

Jami’ar makarantan gaba na Al-Qalam dake jihar katsina ta bayyana cewa hukumar Jami’a ta kasa ta basu lasisi da amincewa wajen gudanar da kosakosai sha uku a matakin digiri na farko.

Meh magana da yawun Jami’ar, Akilu Abubakar ya bayyana ran asabar a jihar katsina cewa hukumar ta NUC ta bada amincewa a takarda ta tura musu na ran 9 ga watan Maris wanda ta iso da sunan shugaban Jami’ar farfesa Nasiru Musa-Yauri.

A takarda wanda wanda yazo da saka hannun maitaimakin shugaban darekta na amincewa, Mista SS Ikani a madadin shugaban hukumar Jami’an kasa farfesa Abubakar Rasheed.
Akilu ya kara bayyana cewa Al-qalam ta yi hazaka matuka wanda hukumar ta yaba dan bada amincewa a watan nowamba da disamba ta shekarar 2022 da ta gabata.

Jami’an Hukumar NUC tayi duba da gudanarwa kosakosai sha uku na Jami’ar, tsakanin social da management science, computing da information sciences, information da natural da applied sciences.

Sakamakon gwajin da hukumar tayi wa makarantar ya nuna kokarinsu a wannan kosakosai sha ukun. Wanda Malam Abubakar ya kirgosu a jere:

Sun hada da Bsc Microbiology, Bsc. Biochemistry, Bsc Science laboratory Technology, Bsc Sociology, Bsc Political science, Bsc Accounting.

Wasu daga ciki sun hada da Bsc business Administration, Bsc Economics, Bsc Software Engineering, Bsc Mathematics, B.E.d Arabic, English da Hausa.

Hukumar Jami’a ta Kasa NUC ta amince wa Jami’ar Alhikmah kosakosai tara (9)

Hukumar da keh kula da tafiyar da jami’an kasa ta baiwa Jami’ar Al-hikmah na jihar kwara Lasisin karin kosakosai guda tara.

Shugaban Makarantar Farfesa Noah Yusuf, ya tabbatar da hakan wa manema labarai a garin Illorin ran Jumma’a.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button