Labaran YauNEWS

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Wanzami A Filin Jirgin Sama

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Wanzami A Filin Jirgin Sama

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wani Wanzami mai suna Nworie Phillip Chikwendu, bisa zarginsa da safarar Hodar Ibilis.

 

DOWNLOAD MP3

Mista Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ne ya tabbatar da hakan acikin sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi, inda sanarwar ta ce, an kama Wanzamin ne a filin tashi da saukar Jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed, a jihar Legas.

Acewar Babafemi, jami’an hukumar sun cafke Nworie ne a filin Jirgin bayan ya dawo daga kasar Brazil a ranar 3 ga watan Mayun 2022 a yayin da jami’an ke cikin tantance kayan matafiyan da su ka iso Nijeriya cikin Jirgin sama na Qatar Airways da ya taso daga Sao Paulo, kasar Brazil zuwa Legas.

Cigaba da garzayowa Labaranyau

DOWNLOAD ZIP

Ya kara da cewa, bayan an binciki jakar Nworie, ya boye hodar Ibilis din ne cikin sannan kuma aka bankado Wasu kayan maye masu nauyin kilogiram 800.

Femi ya ce, Nworie ya yi ikirarin cewa, shi Wanzami ne da yake Aski a Sao Paulo ya kuma shigo Nijeriya ne, don halartar bizne mahaifinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button