Biography

Cikakken Tarihin Umar Namadi, Rayuwarsa, Karatun, Aikinsa, Sana’ar, Siyasarsa, Iyalansa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Umar Namadi 

Labaranyau.com ta kawo bayani kan Tarihin Umar Namadi, karatunsa, aikin sa, siyasar da da sauransu.

Cikakken Tarihin Umar Namadi 
Cikakken Tarihin Umar Namadi

Rayuwar Umar Namadi

Umar Namadi Akanta (accountant) ne kuma dan siyasa wanda aka haifa a kafin Hausa na jihar jigawa a shekarar 1963 ranar 7 ga watan afrailu.

Yayi digirinsa a jami’ar Bayero a jihar kano kuma shine Tsohon mataimakin gwamnan jihar jigawa kuma gwamna mai ci.

Namadi ya kasance musulmi ne kuma dan Jam’iyar APC.

Karatun Umar Namadi

Karatun Umar Namadi 
Karatun Umar Namadi

Umar Namadi yayi karatun firamare dinsa a firamaren gwamnati na kafin Hausa, bayan ya kammala ya wuce Karatun sakandare a Malam Madori kwalajin horas da Malamai inda ya gama da satifiket din Teachers Grade II a shekarar 1982.

A shekarar 1984 ya zauna wa jarabawan A level inda ya samu ya shiga jami’ar bayero kano inda ya gama da digiri kan Accounting a shekarar 1987, ya koma jami’ar bayero yayi digiri ta biyu masters a fannin gudanar da Kasuwanci.

Yana daga cikin kwararrun mambobi na ICAN da kuma Nigeria Institute of Management da kuma Chartered institute of Taxation.

Sana’ar Umar Namadi

Sana’ar Umar Namadi 
Sana’ar Umar Namadi

Tsakanin shekarar 1988 zuwa 1994 namadi ya riqe muqamin Mataimakin odita a kampanin Egwu & Co a jihar Benue.

Yayi aiki da kampanin akanta na Abdu Abdurrahim & Co a jihar kano inda yabada gudumawarsa a fannin audit management da kuma consultancy services.

Ya kasance Principal officer a hukumar National board for community banks kamin ya tafi aiki da kaduna textiles limited.

Namadi ya koma kampanin Dangote inda ya rike muqamin mataimakin janar manaja na kudade da kuma mai kula da shiga da fita na kudi a kampanin sugar na Dangote da kuma Dangote group.

Bayan jimawa da yayi Yana aiki da kampani masu zaman kansu, ya koma aikin gwamnati inda ya riqe muqamin Janar manaja kan finance and account da kuma janar manaja a contribution management department daga shekarar 2006 zuwa 2013.

Ya zama kwararre kan kasuwanci ya kuma kasance managing partner na kampanin Namadi, Umar & Co na Chartered accountants. Kuma ya zama ciyaman na kampanin shinkafa Danmodi food processing limited. Da kuma ciyaman na Danmodi Farms.

Siyasar Umar Namadi

Siyasar Umar Namadi 
Siyasar Umar Namadi

A tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 ya riqe muqamin kwanishinan kudi ta kuma tsare tsare na tattalin Arzikin jihar jigawa.

A shekarar 2019 ya zamo mataimakin gwamna a jihar kuma a shekarar 2023 yayi takara a jam’iyar APC ya kuma lashe zaben, a Yanzu shine gwamna a jihar jigawa. Ya karbi mulki a hannun Tsohon gwamna Abubakar Badaru.

Iyalen Umar Namadi

Iyalen Umar Namadi 
Iyalen Umar Namadi

Namadi ya fito daga cikin gidan ilimi na addinin islama, kakan shi baban mahaifinshi limami ne babba na garin kafin hausa.

Ya kasance musulmi ne mai matukar addini da kuma tsauri wajen kiyaye dokokin addini.

Umar Namadi Yana da aure da kuma yara.

Arzikin Umar Namadi

Arzikin Umar Namadi 
Arzikin Umar Namadi

Umar Namadi Ana kiyasin cewa Yana da arziki kimanin dala miliyan Uku.

Hotunan Umar Namadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button