Biography

Cikakken Tarihin Abubakar Sani Bello, Karatusa, Aikinsa, Karramawa Na Abubakar Sani Bello Siyasarsa, Iyalensa, Arzikinsa, Karramawansa, Korafi Kansa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Abubakar Sani Bello

Abubakar Sani Bello dan siyasa ne a najeriya kuma Tsohon gwamnan Jihar Neja. Ana tunanin yafi kowani gwamna kudi a lokacin da ya zamo gwamna a kasar. Ahalin shi sun kasance suna cikin jadawalin masu kudi na Forbes da kuma najeriya da Afrika. Kasuwancin Ahalin sa sun kushi Kera hanyoyi, harkallar mai, da kuma communication(MTN).

Mahaifinshi yana da kaso 40 cikin dari na kampanin MTN, dan uwanshi ya auri yar Dangote, shi kuma Abubakar yana auren Dr. Amina Abubakar, ya ga Tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar. Kuma mahaifiyar matanshi itace shugaban Alkalai na Jihar Neja.

Cikakken Tarihin Abubakar Sani Bello
Cikakken Tarihin Abubakar Sani Bello

Rayuwar Abubakar Sani Bello

An haifeshi ran 17 ga watan Disamba shekarar 1967. Shine babban dan Attajiri kuma tsohon gwamna Kano a mulkin soja Col Sani Bello. Ya kuma kasance dan jihar neja kuma musulmi ne dan Jam’iyar APC.

DOWNLOAD MP3

Karatun Abubakar Sani Bello

Karatun Abubakar Sani Bello 
Karatun Abubakar Sani Bello

Lolo yayi karatun Firamare a Saint Louis primary school a jihar kano daga shekarar 1974 zuwa 1979. Yayi karatun sakandare a    Makarantar soja (Nigeria Military School zaria) daga 1980 zuwa 1985, ya kuma yi digirinsa a jami’ar maiduguri inda ya karanta tattalin arziki (Economics) daga shekarar 1986 zuwa 1991.

Aikin Abubakar Sani Bello

Aikin Abubakar Sani Bello 
Aikin Abubakar Sani Bello

Abubakar Sani Bello yayi aiki a wurare daban daban manya manya kamar su millennium travels and tours, properties and estates limited, da Heritage Hospitality services limited inda ya riqe muqamai daban daban.

Siyasar Abubakar Sani Bello

Ya shiga siyasa ne inda Abu lolo ya zama Kwamishina na kasuwanci da hannun jari a shekarar 2009 bayan Tsohon gwamnan Neja Aliyu Babangida ya zabe shi, yayi takarar gwamna a jam’iyar APC a shekarar 2015 inda ya lashe zaben kuma ya maimaita a shekarar 2019 ya sauka a 2023.

DOWNLOAD ZIP

Ya kasance mai tausayin talaka inda ya jajirce wajen samar da abubuwa da talaka ke bukata kamar ruwa, asibiti da Makarantu.

Arzikin Abubakar Sani Bello

Arzikin Abubakar Sani Bello 
Arzikin Abubakar Sani Bello

Abubakar Sani Bello mai kudi ne sosai, bincike ta bayyana cewa yana da Arziki kimanin dala Biliyan daya. Ya samu Arzikin sa ne sanadiyar aiki da manyan kampani da kuma siyasa. Kamin ya bar siyasa yayi aiki mai kyau a kampanonin da ya bari inda ya bar zanen aikin sa. Ya riqe muqamin Alternate Darakta a kampanin MTN, Board mamba a broad bank, ciyaman na Prudent Healthcare Management limited da kuma ciyaman Heritage Hospitality Services LTD.

Iyalen Abubakar Sani Bello

Iyalen Abubakar Sani Bello 
Iyalen Abubakar Sani Bello

Abu lolo yana auren Amina Abubakar, diyar Tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Abdulsalam Abubakar. Dakta Amina ta kasance likitan Gynecologist ne a asibitin Barau Dikko a jihar kaduna.

Allah albarkace auren su da yara uku wanda sun hada da Muhammad, Abdulsalam da Maryam.

Korafi Kan Abubakar Sani

Tsohon gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani wanda samari suka kaiwa farmaki kan korafin cewa baya musu aiki, kuma bidiyon farmakin ta shahara a yanan gizo.

Matasan sun kai mai farmaki ne Saboda rashin aiki da kuma yawan zuwa kasar waje domin neman hannun jari wa jihar.

Karramawa Na Abubakar Sani Bello 

Karramawa Na Abubakar Sani Bello 
Karramawa Na Abubakar Sani Bello

Ya samu karramawa daban daban kamar su karramawar UNIMAID Alumni, karramawar Federal Polytechnic Bida Fellowship, Karramawar digirin digirgir a fannin gudanar da kasuwanci Business Administration Daga jami’ar jihar Imo, Owerri.

Hotunan Abubakar Sani Bello

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button