
Chelsea Sun Sayo Cole Palmer Daga Manchester City Akan Kudi £40m
Cole Palmer ya saka hanu a contract na shekara 7 Chelsea tareda ya amincewa da karin shekara, kuma zai jona squad din Chelsea ne tun a wasan su da zasu buga da Nottingham a nan gaba.

Palmer ya buga wasan farko na bude Premier League na wannan season din, wadda Man City suka buga da Burnley, amma ya buga benci a sauran wassi biyun da suka biyo baya.

Ya buga wasanni 25 wa Man City a duka gasannin da suka buga last season, kuma ya samu nasarar cin Premier League da Champions League da kuma FA cup a lokacin.
